Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu yayi alkawarin tallafawa iyalin jami’an tsaro goma Sha daya da Yan bindiga suka halaka a karamar hukumar Shanga da ke jihar Kebbi.

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu yayi alkawarin tallafawa iyalin jami’an tsaro goma Sha daya da Yan bindiga suka halaka a karamar hukumar Shanga da ke jihar Kebbi.

Tinubu ya bayyana hakan ne cikin sakon sa na jaje da ta’aziyya ga iyalai da gwamnatin jihar ta Kebbi game da wannan rashi da akayi na jami’an tsaro.

Shugaban kasar Wanda ya samu wakilcin mataimakin sa Kashim Shettima wajen isar da sakon jaje ga gwamnatin jihar da iyalan mamatan, ya Kuma yi ta’aziyyar rasuwar kakakin majalisar Dokokin jihar Muhammad Usman Zuru.

Da yake Mika Sakon ga gwamnan jihar ta Kebbi a gidan gwamnatin jihar da ke Birnin Kebbi, mataimakin shugaban kasar a madadin shugaba Tinubu ya bayyana wadannan abubuwa biyu da suka faru a matsayin abin damuwa da jajantawa.

Da yake mayar da jawabi, gwamnan jihar ta Kebbi Dr. Nasir Idris bayyana godiyar sa yayi game da wannan ziyarar da tawagar gwamnatin tarayya ta Kai, lamarin da ya bayyana a matsayin halayyar nuna damuwa da shugaban kasa Tinubu ke da shi ga al’uma.

Yace al’umar jihar Kebbi sun kadu da rasuwar shugaban Majalisar dokokin jihar da Kuma jami’an da suka sadaukar da kan su wurin kare rayukan al’umar ta jihar ta Kebbi.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *