Kungiyar NASFAT ta gudanar da addu’o’in musamman domin zaman lafiya da tsaron Najeriya

Kungiyar NASFAT ta gudanar da addu’o’in musamman domin zaman lafiya da tsaron Najeriya

Ƙungiyar Nasrul-Lahi-L-Fatih (NASFAT) ta shirya babban taron addu’o’i na ƙasa da ƙasa domin neman zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Najeriya, tare da roƙon Allah ya kawo ƙarshen matsalolin rashin tsaro da ke damun al’umma.

An gudanar da addu’o’in ne lokaci guda a fiye da rassan ƙungiyar 360 da ke sassa daban-daban na duniya, inda dubban mambobi, malamai da sauran masu ruwa da tsaki suka haɗu wajen neman mafita ta ruhaniya ga ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

Da yake jawabi a yayin taron, Babban Limamin NASFAT, Sheikh Abdul-Azeez Morufu Onike, ya nuna damuwarsa kan yadda matsalolin ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, ta’addanci da sauran ayyukan laifi ke ci gaba da barazana ga zaman lafiyar al’umma.

Ya buƙaci ‘yan Najeriya, musamman al’ummar Musulmi, da su dage wajen yin addu’o’i tare da mara wa ƙoƙarin gwamnati da jami’an tsaro baya domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a faɗin ƙasar nan.

Shehin malamin ya kuma jaddada cewa duk da irin matakan da hukumomin tsaro ke ɗauka, nasarar magance matsalolin tsaro na buƙatar haɗin kai daga jama’a, da rungumar zaman lafiya tare da kaucewa duk wani abu da ka iya haddasa rikici ko tashin hankali.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *