Majalisar Wakilai ta kasa ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman samar da rundunar ’yan sandan jihohi a fadin Najeriya.
An cimma wannan matsaya ne a zaman majalisar na ranar Alhamis bayan tattaunawa kan kudirin mai taken “Kudirin Gyaran Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 domin samar da Rundunar ’Yan Sandan Jiha da sauran batutuwa masu alaka da hakan (Gyara na Shida), 2026.”
Kudirin ya samu gagarumar goyon baya daga mambobin majalisar bayan Mataimakin Kakakin Majalisar kuma Shugaban Kwamitin Gyaran Kundin Tsarin Mulki, Benjamin Kalu, ya gabatar da rahoton kwamitin.
Sakamakon kuri’ar da aka kada ya nuna cewa ’yan majalisa 289 sun amince da kudirin, yayin da mutum daya kacal bai kada kuri’a ba, kuma babu wani dan majalisa da ya nuna adawa da shi.
Sabon tsarin da kudirin ke neman kafawa zai samar da rundunonin ’yan sanda biyu a kasar nan, wato Rundunar ’Yan Sandan Tarayya da kuma Rundunar ’Yan Sandan Jihohi, domin karfafa matakan tsaro da bai wa jihohi damar taka rawa wajen magance matsalolin tsaron yankunansu.
Kudirin ya kuma tanadi yin gyara ga Sashe na 214 na kundin tsarin mulki domin ba wa wadannan rundunoni matsayi na doka.
Haka kuma, Majalisar Dokoki ta Kasa za ta ci gaba da tsara dokoki da ka’idojin gudanar da Rundunar ’Yan Sandan Tarayya, yayin da za a shimfida sharudda da dokokin da za su jagoranci kafa da gudanar da rundunonin ’yan sandan jihohi a fadin kasar.

