A cewar hukumar, mutanen sun kammala dukkan matakan rajista da binciken da ake buƙata kafin a dawo da su Najeriya.
Wadanda suka dawo sun sauka a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas a ranar Alhamis, inda jami’an NEMA tare da wasu hukumomin gwamnati suka tarbe su tare da samar musu da tallafin da ya dace.
Domin sauƙaƙa musu dawowa cikin al’umma, gwamnati ta tanadi motocin da za su kai su zuwa jihohi da wuraren da suka fito a sassa daban-daban na ƙasar.
Haka kuma, an samar da motar asibiti da ma’aikatan lafiya domin kula da duk wanda ke buƙatar taimakon gaggawa ko duba lafiyarsa bayan dawowarsa.
NEMA ta bayyana cewa manufar shirin ita ce tabbatar da cewa dawowar ’yan Najeriya daga ƙasashen waje tana gudana cikin tsari, aminci da mutunci.
Hukumar ta jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki tare da ƙungiyoyi da sauran masu ruwa da tsaki domin tallafa wa waɗanda suka dawo, tare da taimaka musu wajen sake fara rayuwarsu cikin sauƙi a Najeriya.

