Jamhuriyar Nijar na dab da samun sabon tallafin kuɗi daga Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF), bayan da ɓangarorin biyu suka cim ma yarjejeniya a matakin ma’aikata kan ci gaban shirin gyaran tattalin arzikin ƙasar.
An kulla yarjejeniyar ne a yayin ziyarar wata tawagar IMF da ta kai ziyara birnin Yamai tsakanin ranar 2 zuwa 12 ga watan Yuni, a wani ɓangare na nazari na tara da ake yi ƙarƙashin shirin Extended Credit Facility (ECF).
Sai dai kafin a fitar da kuɗaɗen, dole ne Kwamitin Zartarwa na IMF ya amince da yarjejeniyar, kuma ana sa ran hakan zai gudana a ƙarshen watan Yuli. Idan aka amince, Nijar za ta karɓi kusan dala miliyan 33 domin tallafa wa tattalin arzikinta da kuma biyan wasu daga cikin buƙatun kuɗaɗen waje.
IMF ya bayyana cewa tattalin arzikin Nijar ya ci gaba da nuna ƙarfi, inda ya samu bunƙasar kashi 6.9 cikin ɗari a shekarar 2025. Haka kuma ana sa ran bunƙasar za ta kai kashi 7 cikin ɗari a shekarar 2026, musamman saboda ci gaban da ake samu a bangaren noma da kuma albarkatun ƙasa.
Asusun ya kuma yaba da yadda gwamnatin Nijar ke tafiyar da harkokin kuɗaɗenta, yana mai cewa an samu raguwar gibin kasafin kuɗi zuwa kashi 2.9 cikin ɗari na GDP a shekarar 2025. IMF ya danganta wannan nasara da karuwar kuɗaɗen shiga na cikin gida da kuma yawan kuɗaɗen da ake samu daga fitar da man fetur.
Duk da matsalolin tsaro, sauyin yanayi da ƙalubalen samun kuɗaɗe, IMF ya ce Nijar ta samu gagarumin ci gaba wajen inganta tsarin kuɗaɗen gwamnati, rage basussuka da kuma ƙarfafa gaskiya da riƙon amana. Haka kuma ya yaba da matakin da ƙasar ta ɗauka na bayyana wasu kwangilolin man fetur da aka kulla da kamfanoni.
A nata ɓangaren, gwamnatin Nijar ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da za su ƙara kuɗaɗen shiga, bunƙasa shugabanci nagari da kuma samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari da kamfanoni masu zaman kansu.
