Sai dai binciken da aka gudanar ya nuna cewa kaso arba’in da Daya cikin Dari na adadin kudaden sun tafi ga kudaden da ake cirewa wurin raba kudaden da ake baiwa gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomin kasar nan.
Sabon rahoton da Bankin Duniya ya fitar wanda ke fayyace ci gaban da ƙasashe ke samu a fannin kudaden shiga, ya nuna cewa jimillar kudin shigar da Najeriya ta samu a 2023 ya Kai Naira tiriliyan goma Sha bakwai da Biliyan takwas.
Adadin ya karu zuwa Naira tiriliyan ashirin da hudu da Biliyan 45 a shekarar 2024, yayin da kudin ya karu a shekarar 2025 zuwa Naira tiriliyan talatin da bakwai da Biliyan 44.
Jimillar kudaden da aka samu cikin shekarun uku ya haura tiriliyan 83 da Biliyan 97.
Sai dai kudaden da aka cire wurin raba kudaden wata wata na rukunin gwamnatoci uku cikin shekarun ya Kai Naira tiriliyan 34 da Biliyan 53.
Kididdigar ta fayyace cewa, a shekarar 2023 an cire naira tiriliyan 6 da Biliyan 22, inda aka Kuma cire jimillar Naira tiriliyan 13 da Biliyan 38 a 2024, sai Kuma Naira tiriliyan 14 da Biliyan 93 a shekarar 2025.
Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar gibi a kasafin kudin kasar nan, lamarin da gwamnatoci ke bayyana wa a matsayin dalilan karbo bashi daga ciki da wajen kasar nan.
Rahotanni sun nuna cewa bashin da ake bin Najeriya daga ranar 31 ga watan Disambar 2025 ya Kai dalar Amurka Biliyan Dari da goma da digo 3 kwatankwacin naira tiriliyan Dari da hamsin da Tara da Biliyan biyu.

