’Yan sanda sun yi gargadi a Jihar Gombe kan shaye-shaye da rikicin siyasa gabanin 2027.

’Yan sanda sun yi gargadi a Jihar Gombe kan shaye-shaye da rikicin siyasa gabanin 2027.

Rundunar ’yan sanda a Jihar Gombe ta nuna damuwa matuƙa kan yadda shaye-shayen kayan maye da kuma ayyukan ’yan daba masu alaƙa da siyasa ke ƙaruwa, tana mai gargadin cewa lamarin na iya barazana ga tsaro da zaman lafiyar al’umma gabanin zaɓen 2027.

Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Umar Chuso, ne ya bayyana hakan yayin wani taron wayar da kan jama’a da aka gudanar a birnin Gombe, inda ya jaddada buƙatar ɗaukar matakan rigakafi tun kafin matsaloli su ɓarke.

A cewarsa, tsohon tsarin da ’yan sanda ke amfani da shi na kai dauki bayan faruwar laifi kawai ba zai wadatar ba a halin yanzu, yana mai cewa dole ne a mai da hankali kan hana aikata laifi tun daga tushe.

Ya kuma bayyana cewa akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin shaye-shayen kayan maye da aikata laifuka, yana mai misalta su da cewa “tamkar ɗan juma da ɗan jummai ne” wato abu biyu da ke tafiya tare.

Bugu da ƙari, kwamishinan ya yi kira ga ’yan siyasa da su guji rura wutar rikice-rikicen ’yan daba, yana mai cewa hakan na ƙara dagula zaman lafiya a jihar.

A ƙarshe, ya buƙaci al’umma da su haɗa hannu da rundunar ’yan sanda domin tabbatar da tsaro, tare da kiyaye doka da oda a fadin jihar.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *