Mutane biyu sun bayyana cewa tun da farko suna da masaniya kan shirin juyin mulki da aka yi yunƙurin aiwatarwa kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Mutane biyu sun bayyana cewa tun da farko suna da masaniya kan shirin juyin mulki da aka yi yunƙurin aiwatarwa kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Wasu sabbin bayanai sun fito fili a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda mutane biyu daga cikin waɗanda ake zargi da yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu suka amince cewa sun san da shirin tun farko amma ba su sanar da hukumomi ba.

Hakan ya fito ne ta cikin wasu bidiyoyi da masu gabatar da ƙara suka gabatar a kotu, waɗanda suka nuna yadda aka yi wa wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma tambayoyi, ciki har da tsohon kwamandan rundunar sojin ruwa Erasmus Ochegobia Victor da Sufeton ’yan sanda Ahmed Ibrahim.

A cikin bayanansu, Victor ya bayyana cewa ya san wanda ake zargi da jagorantar shirin, har ma ya ce an taɓa neman ya bayar da gudunmawa ta kuɗi da kuma samar da mafaka ga masu shirya juyin mulkin, tare da alƙawarin ba shi muƙami idan aka yi nasara. Sai dai ya ce ya ƙi amincewa, duk da cewa ya ci gaba da hulɗa da su ta hanyar sirri.

Shi kuma Ahmed Ibrahim ya ce da farko an tuntube shi ne kan batun karin girma a aiki, amma daga baya lamarin ya koma tattaunawar kifar da gwamnati. Ya amince cewa ya karɓi kuɗi sama da naira miliyan 1.4, sannan ya taimaka wajen binciken wasu wurare a kusa da Fadar Shugaban Ƙasa, ciki har da ɗaukar hotuna da nazarin hanyoyin shiga.

Bayan haka, ya bayyana cewa masu shirin suna amfani da kalmomin sirri kamar “taki” da “noma” domin ɓoye ainihin ma’anar kuɗi da shirin juyin mulki.

Sai dai a nasa ɓangaren, Manjo-Janar Mohammed Ibrahim Gana mai ritaya ya nesanta kansa daga zargin, yana mai cewa bai san da wani shiri na kifar da gwamnati ba. Ya jaddada cewa tun bayan ritayarsa a 2010 yake rayuwa cikin natsuwa, kuma da ya san da wani abu da ya shafi haka da tuni ya sanar da hukumomi.

Alkalin shari’ar, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, ta ɗage ci gaba da sauraron ƙarar zuwa ranar Talata, 5 ga Mayu domin ci gaba da shari’a.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *