Wasu ’yan bindiga sun kai hari a garin Nding da ke Karamar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato, inda suka hallaka mutum shida, ciki har da mutum biyar daga gida guda.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na dare a ranar Talata, lokacin da maharan suka kutsa cikin garin suka bude wuta kan mazauna yankin.
Wani mazaunin garin, Weng Christopher, ya bayyana cewa mutum biyar daga iyali daya sun mutu nan take, yayin da wani mutum daban shi ma ya rasa ransa a harin.
Ya ce hare-haren sun jefa al’umma cikin tsananin fargaba, inda ya bayyana cewa mutane na rayuwa cikin tsoro sakamakon yadda hare-haren ke yawaita.
Shi ma mai magana da yawun kungiyar matasan Berom, Rwang Tengwong, ya yi Allah wadai da lamarin, yana kira ga jami’an tsaro da su dauki matakin gaggawa domin kawo karshen irin wadannan hare-hare.
Ya kuma bayyana cewa an yi yunkurin kai hari a wani gari mai suna Rim da ke Karamar Hukumar Riyom, amma jami’an tsaro tare da ’yan sa-kai sun samu nasarar dakile harin.
Tengwong ya jaddada bukatar kara kaimi daga hukumomi domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.

Posted inBreaking News Front Page Nigeria Tsaro