Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta samu nasarar dakile wasu hare-haren satar shanu guda biyu a ƙananan hukumomin Igabi da Hunkuyi, inda ta kwato shanu 245 tare da ceto makiyayan da aka yi garkuwa da su yayin harin.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Mansir Hassan, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.
A cewarsa, wasu ’yan bindiga masu ɗauke da makamai sun kai farmaki kan rugar Fulani da ke kusa da ƙauyen Ruby a Ƙaramar Hukumar Igabi. Maharan sun daure makiyayan da igiya kafin su yi awon gaba da dimbin shanunsu.
Bayan samun bayanin lamarin daga shugaban ƙungiyar Miyetti Allah na yankin, rundunar ’yan sanda ta haɗa kai da jami’an bijilanti da kuma dakarun haɗin gwiwa masu kare fararen hula domin bibiyar maharan.
Sanarwar ta ce sakamakon matsin lambar da jami’an tsaro suka yi, ’yan bindigar sun yi watsi da shanun da suka sace tare da tserewa daga wurin. An kwato shanu 245 gaba ɗaya, yayin da aka ceto makiyayan da aka sace ba tare da wata matsala ba.
Rundunar ta ce tana ci gaba da farautar maharan da suka tsere domin gurfanar da su a gaban doka.
