Hukamar INEC Ta Ja Kunnen Jam’iyyu Kan Zabukan Fidda Gwani Bayan Kare Wa’adi.

Hukamar INEC Ta Ja Kunnen Jam’iyyu Kan Zabukan Fidda Gwani Bayan Kare Wa’adi.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa duk wata jam’iyyar siyasa da ta gudanar da zaɓen fidda gwani bayan ranar 30 ga Mayun 2026 na iya fuskantar matsala wajen amincewa da sakamakon, matuƙar ba a samu wani sabon hukunci daga Kotun Ɗaukaka Ƙara da zai sauya matsayin da ake ciki ba.

Kwamishinan hukumar, Mohammed Kudu Haruna, ya ce INEC ta riga ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke, don haka har sai an yanke hukunci a mataki na gaba, ya kamata jam’iyyu su ci gaba da bin ƙa’idojin da Dokar Zaɓe ta 2026 ta tanada.

Tun da farko, wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayyana cewa INEC ba ta da ikon taƙaita ko rage wa’adin da doka ta kayyade dangane da gabatar da sunayen ’yan takara da wasu muhimman matakan zaɓe. Sai dai kuma wata kotun tarayya ta daban ta tabbatar da cewa hukumar na da hurumin tsara jadawalin gudanar da zaɓe, amma cikin iyakar ikon da doka ta ba ta.

A gefe guda kuma, rikice-rikicen da suka biyo bayan zaɓen fidda gwani na jam’iyyar ADC a Kaduna sun sa kwamitin sauraron ƙorafe-ƙorafe ya ba da umarnin sake gudanar da zaɓe a wasu mazabu.

Shugaban kwamitin, Dakta Muhammed Fagge, ya bayyana cewa binciken da suka gudanar ya gano wasu kura-kurai da suka haɗa da cire sunayen wasu masu neman takara daga takardun zaɓe da kuma rashin gamsasshiyar hujja cewa an gudanar da zaɓe a wasu wurare.

A cewarsa, matakin sake zaɓen da aka ɗauka na da nufin tabbatar da adalci, gaskiya da kuma kare martabar tsarin fidda gwani na jam’iyyar.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *