‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 17 a wani Hari da suka kai a Jihar Sakkwato

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 17 a wani Hari da suka kai a Jihar Sakkwato

Akalla mutane 17 ne suka rasa rayukansu bayan da wasu ’yan bindiga suka kai mummunan hari ƙauyen Dangulbi da ke Ƙaramar Hukumar Tureta a Jihar Sakkwato, lamarin da ya girgiza al’ummar yankin a lokacin bukukuwan Sallah.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan, waɗanda adadinsu ya kai kusan 150 kuma suna amfani da babura tare da ɗauke da makamai, sun afka wa ƙauyen da safiyar Lahadi. Sun riƙa harbe-harbe ba tare da zaɓi ba tare da wawashe kayayyaki daga shaguna da gidajen jama’a.

Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun shiga garin ne tsakanin ƙarfe 10 zuwa 11 na safe, inda suka fara bude wuta nan take, abin da ya tilasta wa mazauna ƙauyen tserewa zuwa dazuka domin neman mafaka.

Daga cikin waɗanda suka mutu akwai mutane bakwai da suka je ƙauyen domin gudanar da yawon Sallah. An ce biyar daga cikinsu sun fito ne daga ƙauyen Adarawa a Ƙaramar Hukumar Gummi ta Jihar Zamfara, yayin da sauran biyun suka fito daga Gidan Gambo da ke Ƙaramar Hukumar Shagari a Jihar Sakkwato.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato ya tabbatar da aukuwar harin, inda ya ce jami’an tsaro sun fara gudanar da bincike tare da ɗaukar matakan da suka dace domin daƙile irin waɗannan hare-hare a yankin.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *