Sojoji sun cafke direban mota da ake zargin na safarar miyagun ƙwayoyi zuwa Legas

Sojoji sun cafke direban mota da ake zargin na safarar miyagun ƙwayoyi zuwa Legas

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da kama wani direban mota da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi bayan wani samame da dakarunta suka gudanar a kan hanyar Lagos zuwa Calabar.

A cewar rundunar, an gudanar da aikin ne a ranar 9 ga Yulin 2026 bayan samun sahihan bayanan sirri, lamarin da ya kai ga tare motar tare da kama direban da kuma ƙwace kayayyakin da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa ana shirin kai kayan ne zuwa yankin Berger da ke Jihar Legas. Sai dai wanda aka kama ya kasa bayyana sunan mamallakin kayan ko kuma wanda aka shirya kai wa su.

Rundunar ta ce bayan kammala binciken farko, an miƙa wanda ake zargin tare da kayayyakin da aka ƙwace ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Legas domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakan shari’a.

A halin da ake ciki, Babban Kwamandan Runduna ta 81, Manjo Janar Adebayo Babalola, ya buƙaci jami’an rundunar da su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi da sauran laifuffukan da ke barazana ga tsaron al’umma a yankin da suke kula da shi.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *