Shugaba Tiani zai gana da magadan gari a Maradi kan tsaro da ci gaban Kasar Nijar.

Shugaba Tiani zai gana da magadan gari a Maradi kan tsaro da ci gaban Kasar Nijar.

Shugaban gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, zai jagoranci wani taro da magadan gari a yau Alhamis a birnin Maradi, a wani mataki da ake ganin zai mayar da hankali kan batutuwan tsaro da ci gaban ƙasa.

Wannan shi ne karo na farko da shugaban ƙasar zai gudanar da irin wannan zama kai tsaye da magadan gari tun bayan hawansa mulki sakamakon juyin mulkin shekarar 2023.

Bayan juyin mulkin, gwamnatin sojin Nijar ta naɗa sabbin magadan gari da yawancinsu suka fito daga rundunar soji, ‘yan sanda da kuma jandarma domin jagorantar al’ummominsu.

Ana sa ran taron zai ba shugabannin al’umma damar gabatar da ƙorafe-ƙorafensu tare da jin bayanin matakan da gwamnati ke ɗauka wajen yaƙi da matsalar ta’addanci da ta addabi sassa da dama na ƙasar.

Jamhuriyar Nijar na ci gaba da fuskantar hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, musamman a yankunan karkara, lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro da fararen hula da dama.

A kwanakin baya-bayan nan, hukumomin ƙasar sun ƙara kira ga al’umma da su haɗa kai da jami’an tsaro ta hanyar kai rahoton duk wani motsi ko baƙon da ake zargin zai iya zama barazana ga tsaro.

Taron na Maradi ya zo ne kwana guda bayan shugaban Nijar ya gana da Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergey Lavrov, a Yamai, inda Rasha ta sake tabbatar da goyon bayanta ga Nijar da sauran ƙasashen ƙungiyar AES a ƙoƙarinsu na yaƙi da matsalolin tsaro.

Ana sa ran taron zai fito da muhimman shawarwari kan yadda za a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da shugabannin al’umma wajen magance matsalolin tsaro da bunƙasa ci gaban Nijar.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *