Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila, ya nuna matuƙar damuwa kan zargin kafa wata hukuma ta bogi da aka ce ta samu gurbi a kasafin kuɗin ƙasa, yana mai cewa lamarin abin mamaki ne kuma zai iya bata sunan Nijeriya a idon duniya.
A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Sanatan ya ce bai taɓa tsammanin irin wannan lamari zai faru ba, yana mai bayyana cewa abin ya wuce yadda yake zato.
Kawu Sumaila ya ce kasancewar an saka hukumar cikin kasafin kuɗin gwamnati na nuna cewa akwai mutanen da suka taka rawa wajen aiwatar da hakan, saboda haka ya buƙaci Majalisar Dattawa ta gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda ke da hannu.
Ya bayyana cewa binciken zai taimaka wajen tabbatar da gaskiya tare da ɗora alhakin abin da ya faru kan waɗanda suka aikata hakan.
Sanatan ya ƙara da cewa Majalisar Dattawa na da nauyin tabbatar da gaskiya da kare mutuncin ƙasa, yana mai jaddada cewa tarihi zai yi hukunci kan yadda ‘yan majalisa suka tunkari wannan batu da kuma matakan da suka ɗauka.
