Gwamnatin Rasha ta mayar da martani ga kalaman da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya yi na cewa ɓangarorin da ke rikicin Ukraine ba sa nuna cikakken shirinsu na haɗa kai domin kawo ƙarshen yaƙin.
Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya bayyana mamakinsa kan wannan furuci, yana mai cewa bai dace da irin tattaunawar da ƙasashen biyu suka yi a baya ba. Ya jaddada cewa a wata ganawa da aka gudanar a Alaska a watan Agustan bara, Shugaban Rasha Vladimir Putin ya amince da wasu muhimman shawarwari da Amurka ta gabatar domin samar da zaman lafiya.
Lavrov ya ce duk da sabanin ra’ayoyin da ke tsakanin ɓangarorin biyu, har yanzu akwai damar ci gaba da tattaunawa tsakanin Moscow da Washington, yana mai nuna cewa hanyoyin diflomasiyya ba su rufe ba.
A wani ɓangare kuma, wakilin musamman na Shugaba Putin, Kirill Dmitriev, ya bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Rasha da Amurka kan batun takunkuman tattalin arziƙin da ƙasashen yamma suka kakaba wa Rasha.
Kalaman jami’an Rasha na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da neman hanyoyin rage tashin hankalin da yaƙin Ukraine ya haifar, yayin da ƙasashen duniya ke sa ido kan duk wata alama ta ci gaba a tattaunawar zaman lafiya.

