Gwamnatin Jihar Lagos ta gurfanar da wani jigo na NURTW a gaban babbar kotun jihar da ke Ikeja bisa zargin kashe wani direban babur.

Gwamnatin Jihar Lagos ta gurfanar da wani jigo na NURTW a gaban babbar kotun jihar da ke Ikeja bisa zargin kashe wani direban babur.

Ana tuhumar Oladiti mai shekaru 55 da laifuka uku da suka hada da kisan kai ba da gangan ba, hada baki wajen aikata laifi da kuma yunkurin kisa. Lauyan gwamnati, Jubril Kareem, ya shaida wa kotu cewa an aikata laifukan ne tsakanin watan Agusta da Satumban shekarar 2025 a yankin Lewis Street da ke Lagos Island.

A cewar masu gabatar da kara, Oladiti da wasu da har yanzu ba a kama ba sun hada baki domin aikata laifi, sannan a ranar 17 ga Satumba, 2025, suka yi wa Ramon Imam duka da naushi tare da kai masa hare-hare a kai da fuska, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa. Haka kuma an zarge shi da yunkurin kashe wani mutum mai suna Samuel Omale a watan Agusta ta hanyar dukansa har ya samu munanan raunuka. Sai dai Oladiti ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa a kotu.

Bayan ya musanta laifin, lauyansa, Olanrewaju Ajanaku, ya gabatar da bukatar beli tare da neman a duba lafiyar wanda ake tuhuma. Lauyan gwamnati bai yi adawa da bukatar ba, amma ya bayyana cewa suna son kotu ta umurci gidan gyaran hali da ya tabbatar da halin lafiyar wanda ake zargin. Mai shari’a, Olawale Alebiosu, ya amince da bukatar tare da umurtar gidan yari na Kirikiri ya kai Oladiti asibitin gwamnatin jihar Lagos domin a tantance lafiyarsa. Daga nan kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga Yuni, 2026 domin fara shari’a.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *