Tsohon Ministan Harkokin Waje, Ambassada Yusuf Tuggar, ya yi rashin nassara a zaben fid-da gwani na Jam’iyyar APC a neman  tikitin takarar Gwamnan Jihar Bauchi.

Tsohon Ministan Harkokin Waje, Ambassada Yusuf Tuggar, ya yi rashin nassara a zaben fid-da gwani na Jam’iyyar APC a neman tikitin takarar Gwamnan Jihar Bauchi.

Tuggar, wanda ya sauka daga mukaminsa a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu domin shiga takarar gwamna kafin wa’adin da aka bai wa ministoci ya cika, ya kasa samun rinjaye a zaben da ’yan takara bakwai suka fafata a kai.

Sakamakon zaben da shugaban kwamitin gudanarwa, AIG John Abang mai ritaya, ya bayyana a safiyar Asabar, ya nuna cewa Mohammed Abubakar ne ya lashe zaben da kuri’u 57,517.

Shi kuwa Tuggar ya zo na biyu da kuri’u 26,001, yayin da Nura Manu Soro ya samu matsayi na uku bayan samun kuri’u 13,638.

Sauran ’yan takarar sun hada da Bala Maijama’a Wunti wanda ya samu kuri’u 13,648, Kabir Baba Ma’aji mai kuri’u 8,157, Baba Abubakar Suleiman da ya samu 7,688, sai Yakubu Abdullahi da ya tattara kuri’u 7,181.

Mohammed Abubakar dai ya taba shugabantar Jihar Bauchi kafin ya sha kaye a zaben 2019 a hannun gwamna mai ci yanzu, Bala Mohammed na jam’iyyar PDP.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *