A wajen bikin sanya hannu a Ibadan, gwamnan ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne domin tabbatar da cewa kungiyoyin sintiri da sauran kungiyoyin tsaron al’umma suna aiki ne cikin tsarin doka da zai tabbatar da zaman lafiya da bin doka a jihar.
Makinde ya ce karuwar matsalolin tsaro da yawaitar kungiyoyin da ke gudanar da ayyukan tsaro ba tare da cikakken tsari ba ne ya sa aka samar da wannan doka. Ya bayyana cewa gwamnati na son tabbatar da cewa duk wata kungiyar tsaro ta yi rijista, an tantance ta kuma gwamnati na bibiyarta yadda ya kamata. Haka kuma ya gargadi kungiyoyin zamantakewa da su guji kalaman da za su iya haddasa rikicin kabilanci ko wariya, yana mai jaddada cewa gwamnati ba za ta lamunci aikata laifi da sunan aikin tsaro ba.
Gwamnan ya kuma yi magana kan sace dalibai da malamai da aka yi a karamar hukumar Oriire, inda ya tabbatar wa jama’a cewa gwamnati tare da hukumomin tsaro na aiki tukuru domin ceto wadanda aka sace.
A nasa bangaren, Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Abiodun Aikomo, ya ce duk kungiyar da ke da mambobi sama da mutum biyar dole ne ta yi rijista da ofishin mai ba gwamna shawara kan harkokin tsaro cikin sa’o’i 72 bayan sanya dokar. Ya kara da cewa duk wanda ya karya wannan doka zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.

