Duka ranar 17 ga watan Afrilun kowacce Shekara an ware ta a matsayin ranar Kula da Lafiyar Uwa da Jariri ta Duniya.

Duka ranar 17 ga watan Afrilun kowacce Shekara an ware ta a matsayin ranar Kula da Lafiyar Uwa da Jariri ta Duniya.

An ware ranar ne domin wayar da kai kan muhimmancin kula da lafiyar mata tun daga lokacin ɗaukar ciki har zuwa haihuwa, inda taken bikin na bana ya mayar da hankali kan kawar da ƙalubalen da ke hana mata samun ingantacciyar kulawar lafiya, musamman dangane da lafiyar uwa da jariri.

A nan Kano, jami’an lafiya sun jaddada muhimmancin wannan rana wajen inganta lafiyar al’umma, inda Dakta abubakar Labaran Yusuf, kwamishinan Lafiya na Jihar ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da aiwatar da tsare-tsare masu inganci domin inganta lafiyar mata da ƙananan yara.

Sai dai ya ce duk da waɗannan ƙoƙari, har yanzu akwai ƙalubale, inda a cikin mata dubu ɗari masu haihuwa, kimanin mata 370 ke rasa rayukansu, lamarin da ke nuna buƙatar ƙara zage damtse a ɓangaren kula da lafiyar mata masu juna biyu.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta ƙara ƙaimi wajen tabbatar da cewa babu wata mace da za ta sake rasa ranta yayin haihuwa, ta hanyar inganta asibitoci, ɗaukar sabbin ma’aikata da kuma samar da kayan aiki na zamani domin sauƙaƙa ayyukan jinya.

Haka kuma, Dakta Abubakar Labaran ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su haɗa ƙarfi da ƙarfe tare da buƙatar maza su kula da matansu ta hanyar barinsu su je asibiti domin duba ciki da haihuwa, yayin da rahotanni ke nuna cewa daga cikin mata goma, uku ne kawai ke haihuwa a asibiti, alhali zuwa awo akai-akai na da matuƙar muhimmanci wajen ceton rayukan mata da jariransu.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *