Kotu ta bawa EFCC izinin Kama tsohuwar ministar Jin kan Najeriya

Wata kotu a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, ta bawa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasar ta’annuti EFCC, izinin kama tsohuwar ministar jin ƙai ta ƙasar Sadiya Umar Faruoq.

EFCC na binciken tsohuwar ministar ne da badaƙalar dala miliyan $1.3m da kuma Naira miliyan N746.6m na ma’aikatar da ake zargin an wawure.

A wani saƙo da EFCC ta wallafa a shafinta na X, ta ce mai shari’a Jude Onwuegbuzie, ya kuma ba da izinin kama sakataren ma’aikatar Bashir Nura Alkali.

Ta ce matakin ya biyo bayan ƙin bayyana a gaban kotu da waɗanda ake zargin suka yi a ranar Alhamis.

Lauyan waɗanda ake ƙarar sun buƙaci a ba su uzuri sakamakon rashin lafiya daya hana Sadiya halartar kotun, amma kuma ba a amince da buƙatar tasu ba.

EFCC ta ce ta shigar da ƙarar ce tun a ranar 15 ga watan Disambar 2025, amma ba a samu damar yin ido biyu da waɗanda ake zargin domin miƙa musu takaradar kotun ba.

Sadiya ta riƙe muƙamin ministar ne a mulkin marigayi tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, inda daga baya ta auri tsohon babban hafsan sojin saman Najeriya AVM Sadiq Abubakar.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *