Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya umurci dakarun tsaro da su ƙara ƙaimi wajen murƙushe ‘yan bindiga a yankin arewa maso yamma.

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya umurci dakarun tsaro da su ƙara ƙaimi wajen murƙushe ‘yan bindiga a yankin arewa maso yamma.

Janar Oluyede ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai wa sojojin da ke gudanar da aikin Fansan Yamma a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Ya ce rundunar tsaro na da ƙudirin kawo ƙarshen matsalar ‘yan bindiga a yankin, inda ya nuna cewa matsa musu lamba akai-akai ne kaɗai zai haifar da dawowar zaman lafiya.

Hafsan ya kuma yaba da rawar da gwamnatin Zamfara da al’ummar jihar ke takawa wajen tallafa wa jami’an tsaro a ƙoƙarinsu na tabbatar da tsaro.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *