Hukumar Kula da Birnin Tarayya Abuja (FCTA) ta bukaci Kungiyar Malaman Makarantu ta Najeriya (NUT) reshen Abuja da ta janye yajin aikin da ta fara.

Hukumar Kula da Birnin Tarayya Abuja (FCTA) ta bukaci Kungiyar Malaman Makarantu ta Najeriya (NUT) reshen Abuja da ta janye yajin aikin da ta fara.

Sakataren hukumar kula da ilimi a Abuja, Danlami Hayyo, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai makarantun birnin domin duba halin da ake ciki.

Rahotanni sun nuna cewa tun ranar Juma’ar da ta gabata ne NUT ta umurci malaman firamare da sakandare a Abuja su shiga yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar Litinin.

Kungiyar ta ce matakin ya biyo bayan abin da ta kira sakaci daga hukumomin birnin wajen magance matsalolin malamai, musamman a wannan lokaci na matsin tattalin arziki.

A nasa bangaren, Hayyo ya gargadi cewa ci gaba da yajin aikin na iya shafar daliban da ke shirin fara jarabawar kammala sakandare ta WAEC.

Ya kuma jaddada cewa magance bukatun malaman makarantu na karkashin kananan hukumomi ne da shugabanninsu, ba wai Ministan Abuja Nyesom Wike ba.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *