Fadar shugaban ƙasa ta sanar da cewa an amince da kashe naira biliyan 15 domin fara gina sabon reshe na Makarantar Horar da Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya a Jihar Ogun.
Mashawarcin shugaban ƙasa na musamman kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce matakin ya yi dai-dai da dokar shekarar 2021 da ta kafa makarantar, wadda ta ba ta damar buɗe rassan jami’a a sassa daban-daban na ƙasar.
A cewarsa, shawarar kafa sabon reshen ta samo asali ne bayan tattaunawa tsakanin manyan jami’an gwamnati, ciki har da Ministan Harkokin ‘Yan Sanda, Ministan Ilimi, Babban Sufeton ‘Yan Sanda na ƙasa, da kuma Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC).
Fadar shugaban ƙasa ta ƙara da cewa faɗaɗa makarantar zai taimaka wajen inganta horo na zamani ga ‘yan sanda tare da ƙarfafa tsaron ƙasa baki ɗaya.

