Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta bayyana damuwa kan jinkirin da gwamnatin tarayya ke yi wajen aiwatar da yarjejeniyar shekarar 2025

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta bayyana damuwa kan jinkirin da gwamnatin tarayya ke yi wajen aiwatar da yarjejeniyar shekarar 2025

Shugabannin ASUU na reshen Jami’ar Jos ne suka bayyana hakan, inda suka ce idan gwamnati ba ta ɗauki mataki cikin gaggawa ba, akwai yiwuwar harkokin karatu su tsaya cik a jami’o’in ƙasar.

Ƙungiyar ta ce Majalisar Zartarwa ta ASUU ta ƙasa ta gudanar da taro a Jami’ar Modibbo Adama a ranakun 9 da 10 ga watan Mayun 2026 domin duba yadda ake aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakaninta da gwamnatin tarayya a ranar 23 ga watan Disambar 2025.

ASUU ta nuna rashin jin daɗinta kan abin da ta kira rashin ƙwazo daga gwamnati wajen cika alkawurran da ke cikin yarjejeniyar, tana mai cewa hakan na ƙara tayar da hankali a tsakanin malaman jami’o’i.

Ƙungiyar ta kuma yi zargin cewa har yanzu gwamnatin tarayya ba ta kafa kwamitin da zai kula da aiwatarwa da kuma sanya ido kan yarjejeniyar ba, duk da cewa an amince da hakan domin tabbatar da tafiyar komai yadda ya kamata.

ASUU ta yi gargaɗin cewa idan aka ci gaba da nuna halin ko-in-kula, hakan na iya haifar da sabon yajin aiki a faɗin jami’o’in Najeriya.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *