Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ɗaukar matakai masu ƙarfi har sai an dawo da cikakken zaman lafiya da tsaro a faɗin Najeriya.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ɗaukar matakai masu ƙarfi har sai an dawo da cikakken zaman lafiya da tsaro a faɗin Najeriya.

Tinubu ya bayyana hakan ne a Abuja, inda ya nuna cewa matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta a halin yanzu za su ragu a hankali har su zama tarihi.

Shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa na bai wa kare rayuka da dukiyoyin al’umma muhimmanci, yana mai tabbatar da cewa ana ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro.

Ya ƙara da cewa alhakin kare duk wani ɗan Najeriya yana kansa a matsayin shugaban ƙasa, lamarin da ya sa gwamnati ke ci gaba da ƙarfafa rundunonin tsaro, ciki har da sojoji da ‘yan sanda, tare da ƙarfafa haɗin kai tsakaninsu da jama’a.

Tinubu ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa Najeriya za ta yi nasara a yaƙin da take yi da ‘yan bindiga tare da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkan sassan ƙasar.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *