Rundunar Sojin Najeriya ta yi gargaɗi ga al’umma kan yiwuwar hare-haren mayaƙan Boko Haram da ISWAP a lokacin bukukuwan Babbar Sallah.

Rundunar Sojin Najeriya ta yi gargaɗi ga al’umma kan yiwuwar hare-haren mayaƙan Boko Haram da ISWAP a lokacin bukukuwan Babbar Sallah.

A wata sanarwa da hedikwatar rundunar ta fitar, ta bayyana cewa bayanan sirri da aka samu sun nuna cewa ƙungiyoyin biyu na iya amfani da lokacin shagulgulan Sallah wajen kai hare-hare kan fararen hula, musamman a wuraren da jama’a ke taruwa.

Rundunar ta ce an riga an baza dakarun soji a wuraren da ake ganin na da haɗari a sassan yankin domin ƙarfafa tsaro, tare da amfani da kayan tattara bayanan sirri domin gano duk wata barazana tun kafin ta afku.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa an ƙara yawan sintiri da kuma haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro, ƙungiyoyin JTF da masu aikin sa-kai domin tabbatar da zaman lafiya a lokacin bikin.

Sojin sun shawarci mazauna yankin da su kasance cikin lura tare da rage zirga-zirgar da ba ta zama dole ba, musamman da daddare ko a wuraren da babu jami’an tsaro.

Haka kuma rundunar ta buƙaci jama’a su gudanar da bukukuwan Sallah a kusa da muhallansu, su guji cunkoson manyan taruka, sannan su riƙa kai rahoton duk wani motsi ko mutum da suke zargi ga jami’an tsaro ba tare da ɓata lokaci ba.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *