Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta sanar da nasarar ceto Misis Busayo Adelabu-John Paul tare da ’ya’yanta tagwaye masu shekara 12, Peter da Paul, bayan kwanaki da aka yi garkuwa da su a birnin Ibadan na jihar Oyo.
A cewar kakakin rundunar, DCP Anthony Placid, an samu nasarar ceto su ne sakamakon wani samame da jami’an sashen leƙen asiri suka kai maboyar masu garkuwa da mutane bayan tattara sahihan bayanan sirri da gudanar da bincike mai zurfi.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun yi artabu da masu garkuwar a yayin aikin, inda aka kashe mutum biyu daga cikin waɗanda ake zargi tare da kwato bindigogi guda biyu.
Rundunar ta bayyana cewa matar da tagwayen nata sun kuɓuta lafiya ba tare da sun samu wani rauni ba, kuma an kai su domin duba lafiyarsu bayan ceton.
Haka kuma, ’yan sanda sun tabbatar da cewa ana ci gaba da neman sauran waɗanda suka tsere daga wajen domin cafke su tare da gurfanar da su a gaban kotu.
An sace Misis Busayo Adelabu-John Paul da ’ya’yanta ne a ranar 3 ga watan Yuni yayin da take kan hanyar kai yaran makaranta a birnin Ibadan, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma kafin wannan nasarar ceto da jami’an tsaro suka samu.

