Wasu ’yan bindiga sun harbe Hakimin Gwande da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato, Saf Samuel Alaket, har lahira.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata yayin da hakimin ke dawowa gida daga taron Majalisar Sarakunan Gargajiya da aka gudanar a Bokkos. Rahotanni sun ce maharan sun yi masa kwanton-ɓauna a kusa da iyakar Sha da Daffo.
An garzaya da shi asibiti bayan ya samu munanan raunuka, amma daga bisani ya rasu yayin da ake masa magani.
Mazauna yankin sun bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga al’ummar Gwande da yankin Bokkos baki ɗaya. Haka kuma, shugaban matasan Bokkos, Christopher Luka, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa harin ya jefa jama’a cikin fargaba.
Sai dai ya ce shugabannin al’umma sun yi ƙoƙarin kwantar da hankalin jama’a, kuma yankin ya ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan Jihar Filato ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba.

