Yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Amurka da Iran domin kawo ƙarshen rikicin yaƙi ta haifar da sabon ƙalubale ga Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, inda ta girgiza wasu daga cikin manyan manufofin siyasar gwamnatinsa.
Netanyahu, wanda ya shahara da kusancinsa da shugabannin Amurka da kuma tasirinsa a harkokin tsaron yankin Gabas ta Tsakiya, ya samu kansa cikin yanayi mai sarkakiya bayan yarjejeniyar, wadda da alama an tsara ta ba tare da cikakken tasirin Isra’ila ba.
Masana harkokin siyasa na ganin wannan mataki na iya nuna raguwar karfin da Isra’ila ke da shi wajen rinjayar manufofin Washington, musamman kan batun Iran da Netanyahu ya dade yana dauka a matsayin babbar barazana ga tsaron kasarsa.
Duk da cewa Isra’ila ta dade tana neman matsin lamba mai tsauri kan Iran, yarjejeniyar ta kawo karshen rikicin ba tare da cika wasu daga cikin muhimman bukatun Tel Aviv ba, lamarin da ya jawo muhawara kan ko Isra’ila ta cimma abin da take nema.
A gefe guda kuma, wasu masu lura da al’amura na ganin Iran ta samu damar fita daga rikicin cikin yanayi mai karfi fiye da yadda aka yi hasashe, yayin da Isra’ila ke fuskantar tambayoyi kan nasarorin da ta samu.
Haka kuma, matsin lambar da ke tasowa daga Amurka da Iran na neman dakatar da rikicin Hezbollah a Lebanon na kara dagula lamarin ga Netanyahu, musamman a lokacin da yake fuskantar muhimman kalubalen siyasa a cikin gida da kuma shirye-shiryen zabuka masu zuwa.
