Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana aniyarsa ta yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da an kuɓutar da ɗalibai da malamai 46 da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Oriire a ranar 15 ga watan Mayu.
Makinde ya yi wannan bayani ne a ranar Talata lokacin da ya karɓi masu zanga-zangar da fitaccen mai fafutuka a shafukan sada zumunta, Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan, ya jagoranta zuwa gidansa da ke Ikolaba a birnin Ibadan.
An gudanar da zanga-zangar ne domin nuna damuwa kan yadda matsalar rashin tsaro da sace-sacen mutane ke ci gaba da ƙaruwa a jihar, musamman lamarin sace ɗaliban makaranta tare da malamansu.
Yayin da yake jawabi ga masu zanga-zangar, gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na aiki kafada da kafada da jami’an tsaro domin ganin an ceto waɗanda aka sace cikin koshin lafiya, yana mai jaddada cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai an cimma wannan buri.
Makinde ya kuma yaba da ƙoƙarin jami’an tsaro, yana cewa sun nuna jajircewa da sadaukarwa wajen gudanar da ayyukan ceto, inda ya bayyana cewa wasu daga cikin jami’an sojin da ke cikin aikin sun rasa rayukansu a yayin gudanar da wannan aiki.

