An kashe mutum ɗaya a Kenya bayan rikici ya ɓarke tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar adawa da gina wata cibiyar killace masu cutar Ebola a garin Nanyuki.
Zanga-zangar ta gudana ne a kusa da sansanin sojojin saman Laikipia, inda ake gina cibiyar da za ta karɓi ’yan ƙasar Amurka da za su dawo daga Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (DRC), ƙasar da ke fama da ɓarkewar cutar Ebola.
Rahotanni sun nuna cewa masu zanga-zangar sun toshe hanyoyi tare da kunna tayoyi, yayin da jami’an ’yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye da ruwan zafi domin tarwatsa taron. A yayin rikicin ne aka ji karar harbe-harbe, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda.
Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce wani mutum ya samu matsalar numfashi sakamakon shakar hayaki mai sa hawaye, yayin da aka kama wasu da dama a lokacin tarzomar.
Yawancin mazauna yankin na nuna damuwa kan shirin gina cibiyar, suna masu cewa Kenya ba ta taɓa fuskantar ɓarkewar cutar Ebola ba, don haka bai kamata a kawo masu ɗauke da cutar cikin ƙasar ba.
Wata mazauniyar yankin, Priscilla Waimani, ta bayyana cewa al’ummar Laikipia ba sa son yankinsu ya zama wurin da za a keɓe masu fama da irin wannan cuta mai haɗari.
Ana sa ran cibiyar mai gadaje 50 za ta kula da mutanen da ke buƙatar killacewa, kuma rahotanni sun nuna cewa aikin ginin ya kusa kammaluwa duk da umarnin kotu na dakatar da shi na wani ɗan lokaci da kuma adawar wasu shugabannin yankin.
A gefe guda, gwamnatin Shugaba William Ruto ta dage kan cewa aikin yana da muhimmanci ga tsarin kariyar lafiya na ƙasar, tana mai nuna cewa Kenya da Amurka sun daɗe suna haɗin gwiwa a fannin lafiya tsawon shekaru da dama.
Gwamnatin Amurka ta yi alƙawarin bayar da tallafin dala miliyan 13.5 domin ƙarfafa shirye-shiryen yaƙi da cutar Ebola a Kenya.
Sai dai masu zanga-zangar na ci gaba da kira da a dakatar da aikin, suna masu cewa ya kamata a mayar da hankali kan magance matsalolin lafiya da ke fuskantar ’yan Kenya kafin karɓar irin wannan shiri daga ƙasashen waje.
