Wani matashi mai yi wa kasa hidima ana zarginsa da Hallaka Mahaifinsa ta hanyar daba masa wuka.

Wani matashi mai yi wa kasa hidima ana zarginsa da Hallaka Mahaifinsa ta hanyar daba masa wuka.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da mahaifin, Mista Adimike Godwin, ya ziyarci dansa daga Legas domin duba halin da yake ciki.

An ce mahaifin ya nuna rashin jin dadinsa kan wasu dabi’u da ya lura da su daga wajen dan nasa, lamarin da ya haifar da takaddama a tsakaninsu.

Shaidu sun bayyana cewa rikicin ya barke ne da daddare bayan matashin ya dawo daga wani wajen shakatawa, inda tambayoyin da mahaifin ya yi suka rikide zuwa cacar baki.

A yayin hatsaniyar ne ake zargin matashin ya dauko wuka ya kai wa mahaifinsa hari, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.

Rundunar ’yan sandan Abuja ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa jami’anta sun isa wurin bayan samun kiran gaggawa, inda suka tarar da mutumin kwance cikin jini.

An garzaya da shi asibiti, amma likitoci sun tabbatar da cewa ya rasu kafin samun ceto.

Mai magana da yawun rundunar, SP Josephine Adeh, ta ce an tsare mutane biyar domin taimakawa bincike, ciki har da wani dan uwan mamacin.

Ta kara da cewa Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, Ahmed Muhammed Sanusi, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *