Masu neman Takarar Gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC a wasu jihohin Najeriya sun nuna rashin amincewa da tsarin sasanci da shugabannin jam’iyyar ke ƙoƙarin aiwatarwa kafin zaɓen 2027.

Masu neman Takarar Gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC a wasu jihohin Najeriya sun nuna rashin amincewa da tsarin sasanci da shugabannin jam’iyyar ke ƙoƙarin aiwatarwa kafin zaɓen 2027.

Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla jihohi 10 ne ke fama da rikici tsakanin masu neman takara da shugabannin jam’iyyar, duk da ƙoƙarin da gwamnoni da wasu jiga-jigan APC ke yi na samar da ɗan takara guda domin kauce wa rabuwar kai.

Jihohin da ake fama da wannan takun saka sun haɗa da Kwara, Gombe, Oyo, Adamawa, Bauchi, Plateau, Lagos, Nasarawa, Rivers da Yobe, inda ake zargin wasu ‘yan takara sun ƙi janyewa duk da matsin lamba da ake musu.

A gefe guda kuma, APC ta sanya kudin fom ɗin neman takarar gwamna a kan Naira miliyan 10, yayin da fom ɗin tsayawa takara ya kai Naira miliyan 40.

Bayanai sun nuna cewa jam’iyyar ta samu sama da Naira biliyan 5 daga siyar da fom ga masu neman takara sama da 100 a faɗin Najeriya.

Ana sa ran APC za ta gudanar da zaɓen fidda gwani a jihohi 28 ranar 21 ga watan Mayu, musamman a wuraren da sulhu tsakanin ‘yan takara bai yi nasara ba.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *