Tsohon shugaban Najeriya  Janar Yakubu Gowon mai ritaya, ya gargadi masu neman mulki da sauran ’yan siyasa kan dasu guji Kausasan Kalamai yayin gudanar da Kamfe.

Tsohon shugaban Najeriya Janar Yakubu Gowon mai ritaya, ya gargadi masu neman mulki da sauran ’yan siyasa kan dasu guji Kausasan Kalamai yayin gudanar da Kamfe.

Ya bayyana hakan ne a babban birnin tarayya Abuja yayin bikin ƙaddamar da littafin rayuwarsa mai suna “My Life of Duty & Allegiance”, wanda Havilah Group ta wallafa.

Gowon, wanda ya shugabanci ƙasar tsakanin 1966 zuwa 1975, ya nuna kwarin gwiwar cewa duk da matsalolin tattalin arziki da na tsaro da ake fama da su, Najeriya za ta ci gaba da dorewa cikin haɗin kai.

A wajen taron, Bishop Matthew Kukah na Sokoto ya gabatar da sharhi kan littafin, yayin da Janar Theophilus Danjuma mai ritaya ya jagoranci sayen kwafin littafin kan kuɗin da suka kai naira biliyan uku.

Tsohon shugaban ya ce shekarar 2026 na da muhimmanci sosai domin ta cika shekaru 60 tun bayan shigar sojoji cikin harkokin mulkin Najeriya da kuma shekaru 60 da shi kansa ya hau kan mulki a wani lokaci da ƙasar ke cikin mawuyacin hali.

Haka kuma, ya yi kira ga ’yan siyasa da su gudanar da siyasa cikin lumana tare da guje wa duk wani abu da zai iya kawo barazana ga dimokuraɗiyya ko haɗin kan Najeriya kafin zaɓen 2027.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *