Hukumar FCC ta bayyana cewa za ta ɗauki tsauraran matakai kan duk wata ma’aikata ko hukuma da ta karya dokokin ɗaukar aikin Gwamnati.

Hukumar FCC ta bayyana cewa za ta ɗauki tsauraran matakai kan duk wata ma’aikata ko hukuma da ta karya dokokin ɗaukar aikin Gwamnati.

Shugabar hukumar, Hajiya Ayo Omidiran, ta ce duk wani jami’i da aka samu da laifin karya ƙa’idojin ɗaukar ma’aikata ko kauce wa tsarin da doka ta tanada, zai iya fuskantar hukunci a gaban kotu.

Ta bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka shirya domin sanar da sababbin dokokin ɗaukar aiki a ma’aikatun gwamnatin tarayya. Sanarwar ta fito ne ta bakin mai magana da yawun hukumar, Ademola Lawrence.

FCC ta ce sabon tsarin an ƙirƙire shi ne domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen rabon ayyukan gwamnati, tare da tabbatar da cewa dukkan jihohi da yankuna sun samu damar wakilci yadda ya kamata.

Sabbin dokokin sun tanadi cewa duk wata hukuma da ke son ɗaukar ma’aikata sama da mutum 125 dole ne ta fara tallata guraben aikin a jaridun ƙasa biyu da kuma shafin hukumar na tsawon makonni shida.

Har ila yau, an umurci ma’aikatu da hukumomi su sanar da FCC kafin su fara tallan aikin da makonni biyu, sannan jami’an hukumar su kasance wajen sa ido yayin tantance masu neman aikin.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *