Sojoji sun kashe ’yan bindiga tare da ceto mutane da dabbobi a Sokoto, Katsina da Kaduna

Sojoji sun kashe ’yan bindiga tare da ceto mutane da dabbobi a Sokoto, Katsina da Kaduna

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation FANSAN YAMMA sun samu gagarumar nasara a wasu hare-hare da suka kai a jihohin Sokoto, Katsina da Kaduna, inda suka kashe wasu ’yan bindiga, suka ceto mutanen da aka yi garkuwa da su tare da ƙwato dabbobi da makamai.

A wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa a jihar Sokoto, dakarun sun dakile wani yunkurin hari da ’yan bindiga suka shirya kai wa garin Tureta bayan samun sahihan bayanan sirri kan motsinsu, lamarin da ya tilasta musu tserewa daga yankin.

Sanarwar ta ce bayan da maharan suka tsere, jiragen yaƙin sojoji sun bi sawunsu har zuwa ƙauyen Sulubawa Gidan Kare, inda aka kai farmaki kan maboyarsu. A yayin farmakin, an kuɓutar da wasu daga cikin mutanen da aka sace tare da ƙwato shanu da aka yi awon gaba da su, duk da cewa dakarun sun fuskanci turjiya da kwanton ɓauna daga ’yan ta’addan.

A jihar Katsina kuma, sojojin sun kai samame a wani sansanin ’yan ta’adda da ke ƙaramar hukumar Matazu da safiyar ranar 22 ga Yunin 2026. Rahotanni sun nuna cewa an kashe ’yan bindiga biyu a yayin harin, yayin da wasu da dama suka tsere dauke da raunuka.

Haka zalika, a jihar Kaduna, dakarun sun yi nasarar hallaka wasu ’yan bindiga biyu da ake zargi da yunƙurin satar shanu. Sun kuma ƙwato makamai da kuma dabbobin da aka sace daga hannun maharan.

Rundunar ta jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukan sintiri da farmaki domin dakile ayyukan masu aikata laifuka da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a yankunan da matsalar tsaro ta fi kamari.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *