Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa matakin da Amurka ta ɗauka na rage yawan ma’aikatanta a ofishin jakadancinta da ke Najeriya ba ya da alaƙa kai tsaye da matsalolin cikin gida .

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa matakin da Amurka ta ɗauka na rage yawan ma’aikatanta a ofishin jakadancinta da ke Najeriya ba ya da alaƙa kai tsaye da matsalolin cikin gida .

Ya bayyana hakan ne a Abuja yayin kaddamar da sabuwar hedikwatar Hukumar Ayyukan Majalisar Dokoki ta Ƙasa, inda ya yi tsokaci kan rahotannin da ke cewa wasu ƙasashe na rage ayyukan jakadancinsu a Najeriya.

Akpabio ya ce irin wannan mataki ba Najeriya kaɗai ya shafa ba, yana mai jaddada cewa wasu ƙasashe na ɗaukar irin waɗannan matakai ne bisa la’akari da yanayin tsaron duniya baki ɗaya, musamman dangane da rikice-rikicen ƙasa da ƙasa da ke gudana.

Ya kuma musanta zargin da ke cewa lamarin yana da alaƙa da siyasar cikin gida ko kuma zaɓukan da ke tafe a Najeriya, yana mai cewa matakin ya fi alaƙa da tsaro na duniya fiye da batutuwan cikin gida.

A baya dai, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayar da izinin ficewar wasu ma’aikatan gwamnati da ba su da muhimman ayyuka tare da iyalansu daga ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja, tana mai danganta hakan da matsalolin tsaro.

Haka kuma, a cikin sabon gargadin tafiye-tafiye da aka fitar a makon da ya gabata, an shawarci ‘yan Amurka da su sake tunanin zuwa Najeriya daga ranar 8 ga Afrilu, 2026, sakamakon barazanar ta’addanci da sauran matsalolin tsaro.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *