Shugaban kasa Bola Tinubu zai kai ziyarar aiki zuwa ƙasashe uku Kenya,Rwanda da Faransa.

Shugaban kasa Bola Tinubu zai kai ziyarar aiki zuwa ƙasashe uku Kenya,Rwanda da Faransa.

Wannan saƙon na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Bayo Onanuga ya fitar, inda ya ce shugaban zai bar Najeriya ne a yau Asabar 2 ga watan Mayu.

Shugaban zai fara sauka a Faransa daga can sai ya tafi Nairobi, inda zai halarci taron haɗakar Faransa da ƙasashen Afirka wanda Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Kenya William Ruto za su jagoranta.

Sanarwar ta ce za a gudanar da taron ne kan hanyoyin inganta kasuwancin zamani da makamashi da canjin yanayi da sauran abubuwa masu muhimmanci.

Sanarwar ta ƙara da cewa bayan taron ne Tinubu zai tafi Kigali na ƙasar Rwanda domin halartar taron manyan shugabannin gudanarwar kamfanoni na Afirka wanda za a yi a ranakun 14 da 15 ga watan Mayu, inda a cewarsa daga can zai koma Najeriya.

 

 

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *