Wata guguwa mai tsanani ta lalata gidaje da dama a Jihar Jigawa.

Wata guguwa mai tsanani ta lalata gidaje da dama a Jihar Jigawa.

Wata mahaukaciyar iska mai ɗauke da ruwan sama ta haddasa mummunar ɓarna a wasu sassan birnin Dutse na Jihar Jigawa, inda aka kiyasta cewa sama da gidaje 3,500 ne suka lalace ko suka rushe.

Bala’in, wanda ya afku a daren Asabar, ya fi shafar yankunan Kwaimawa, Dan Masara, Rungumau da Takur Aduwa, inda gidaje, shaguna, masallatai da kayayyakin wutar lantarki suka samu matsananciyar illa.

Mazauna yankunan sun bayyana lamarin a matsayin ɗaya daga cikin mafi munin bala’o’in iska da suka taɓa gani a cikin shekaru da dama. Sun ce mutane da yawa sun rasa matsugunansu, yayin da dukiyoyin da suka kai miliyoyin naira suka salwanta cikin ɗan lokaci.

Wasu mazauna yankin sun ce iskar ta yaye rufin gidaje, ta rushe katangu tare da lalata tashoshin ruwa da kayayyakin more rayuwa. Haka kuma motoci da dama sun lalace sakamakon faɗuwar tarkacen gine-gine da itatuwa.

Duk da girman ɓarnar da aka yi, babu rahoton rasa rai, sai dai an samu mutane da dama da suka jikkata yayin da wasu gidaje suka rushe a lokacin da mazaunansu ke ciki.

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA) ta ce ta fara tantance girman asarar domin gano waɗanda bala’in ya shafa da kuma irin tallafin da za a ba su.

Hukumar ta kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta tanadi kayayyakin agaji da kayan gine-gine domin tallafa wa iyalan da gidajensu suka lalace yayin da suke ƙoƙarin farfaɗo da rayuwarsu.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *