An Kashe Matashin da ya hallaka mahaifinsa kar rashin abinci a Jihar  Edo.

An Kashe Matashin da ya hallaka mahaifinsa kar rashin abinci a Jihar Edo.

Wani rikici da ya samo asali daga rashin abinci ya rikide zuwa mummunan lamari a Jihar Edo, inda wani matashi mai suna Pere Odese mai kimanin shekaru 30 ya kashe mahaifinsa, Friday Odese.

Al’amarin ya faru ne a ƙauyen Ikhehe da ke yankin Ewato a Ƙaramar Hukumar Esan ta Kudu maso Yamma a Jihar Edo.

Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa rikicin ya fara ne bayan mahaifin ya shaida wa ɗansa cewa babu abinci a gida, tare da bayyana cewa rashin tsaro da barazanar ’yan bindiga sun hana shi zuwa gona domin neman abinci.

Ana cikin takaddamar ne matashin ya ɗauki adda ya kai wa mahaifin hari, lamarin da ya yi sanadin rasuwarsa nan take.

Wani maƙwabcin da ya yi yunƙurin shiga tsakani ya samu raunuka, kuma ana kula da shi a asibiti.

Bayan aukuwar lamarin, matashin ya yi ƙoƙarin guduwa daga yankin, sai dai fusatattun mazauna garin suka bi sawunsa suka kama shi, inda suka lakaɗa masa duka har ya mutu.

Lamarin ya jawo asarar rayukan mahaifi da ɗa a lokaci guda.

Rundunar ’yan sandan Jihar Edo ta tabbatar da samun bayanai kan aukuwar lamarin, sai dai ta ce har yanzu ba a shigar da rahoto a hukumance ba.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *