Kwalejin Horar da Sojoji ta Najeriya (NDA) ta bayyana rashin amincewarta da wani ƙudirin gyaran doka da ke neman a bai wa ɗaliban da suka kammala karatu a makarantun sakandaren soji damar samun gurbin shiga kwalejin kai tsaye.
Hukumar ta ce aiwatar da irin wannan tsari na iya kawo cikas ga manufar bai wa dukkan yankunan ƙasar damar samun wakilci daidai wa daida, tare da rage damar sauran ɗaliban da suka cancanci shiga ta hanyar gasa.
Daraktan Horarwa na NDA, Birgediya Janar Taiye Ahmed, ne ya bayyana wannan matsaya a ranar Talata yayin wani taron sauraron ra’ayoyin jama’a da Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai ya gudanar.
A yayin taron, an yi nazari kan ƙudurrin dokoki guda huɗu da suka shafi bangaren tsaro, ciki har da kudirin gyara dokar NDA na shekarar 2024 wanda ke neman bai wa ɗaliban makarantun soji damar shiga kwalejin ba tare da bin tsarin gasa da ake amfani da shi ga sauran masu neman shiga ba.
Ahmed ya bayyana cewa ƙudirin na neman sauya Sashe na 8(2) na Jadawali na Biyu na dokar NDA, domin bai wa ɗaliban makarantun soji damar samun shiga kai tsaye, lamarin da ya ce na iya haifar da rashin daidaito wajen ba da damar shiga kwalejin.

