Manyan Shuwagabannin kamfanonin  da makamashi na Najeriya  sun bayyana goyon baya ga Tinubu a babban Zaben 2027.

Manyan Shuwagabannin kamfanonin da makamashi na Najeriya sun bayyana goyon baya ga Tinubu a babban Zaben 2027.

Wasu fitattun shugabannin kamfanonin da ke aiki a fannonin injiniya da makamashi sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da nuna gamsuwa da matakan gyaran tattalin arziki da gwamnatinsa ke aiwatarwa.

A yayin wata ganawa da suka yi a Abuja, shugabannin kamfanonin sun bayyana cewa suna da kwarin gwiwar cewa manufofin da gwamnatin Tinubu ta bullo da su za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa a Najeriya.

Sun kuma yi alƙawarin bayar da tallafin da ya haɗa da kayan aiki, kuɗaɗe da sauran gudunmawar da za su taimaka wajen aiwatar da shirye-shiryen ci gaban ƙasa, musamman a ɓangarorin makamashi da injiniya.

A cewarsu, wannan haɗin gwiwa alama ce ta yadda masu zuba jari da manyan kamfanoni ke ƙara amincewa da alkiblar tattalin arzikin Najeriya da kuma makomarta.

Da yake nasa jawabin, Darakta Janar na RTIFN, Ahmed Bala, ya yaba da irin goyon bayan da kamfanonin suka nuna, yana mai cewa hakan zai ƙara taimakawa wajen faɗakar da jama’a kan manufofi, ayyuka da nasarorin gwamnatin Tinubu, tare da bayyana irin ribar da al’umma za su samu daga aiwatar da su.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *