Jam’iyyar ADC ta naɗa kwamitin wucin gadi bayan sauke shugabannin ta na Jihar Kano.

Jam’iyyar ADC ta naɗa kwamitin wucin gadi bayan sauke shugabannin ta na Jihar Kano.

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta sanar da sauye-sauye a tsarin shugabancinta na Jihar Kano, inda ta rushe tsohon shugabancin jihar tare da kafa kwamitin riƙon ƙwarya domin tafiyar da harkokin jam’iyyar na ɗan lokaci.

Mataimakiyar Shugabar ADC ta Ƙasa mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, Hajiya Najaatu Muhammad, ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Kano.

A cewarta, an zaɓi Alhaji Umar Bala domin jagorantar sabon kwamitin riƙon ƙwaryar da aka kafa, wanda zai kula da harkokin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a gudanar da sabon zaɓen shugabanni a jihar.

Najaatu Muhammad ta ce matakin ya samu amincewar shugabancin jam’iyyar na ƙasa kuma ya yi daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin ADC.

Ta bayyana cewa manufar sauyin ba wai nuna goyon baya ga wani ɓangare ba ne, sai dai samar da yanayin da zai ba jam’iyyar damar ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin tsari da kwanciyar hankali.

Ta ƙara da cewa kafa kwamitin riƙon ƙwarya zai taimaka wajen magance matsalolin shugabanci da suka taso tare da tabbatar da daidaito a tafiyar jam’iyyar a Kano.

Haka kuma ta yabawa mambobi da magoya bayan ADC a jihar bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen bunƙasa jam’iyyar, tana mai jaddada cewa shugabancin ƙasa na jam’iyyar na mutunta sadaukarwa da jajircewar da suka nuna tsawon lokaci.

Sabon kwamitin zai ci gaba da tafiyar da harkokin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a kammala shirye-shiryen gudanar da zaɓen sabbin shugabanni a Jihar Kano.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *