Cibiyar Kare Muradun Musulmi ta Najeriya (MPAC) ta nuna rashin amincewarta da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Ibadan wanda ya soke hukuncin wata babbar kotun Jihar Oyo da ta bai wa ɗalibai mata Musulmai damar sanya hijabi a Makarantar International School, Ibadan (ISI).
A wata sanarwa da cibiyar ta fitar, ta bayyana cewa batun bai tsaya kan dokar kayan makaranta kaɗai ba, illa dai yana da alaƙa da kare haƙƙin addini da kuma ’yancin ɗalibai mata Musulmai na yin suturar da addininsu ya tanada.
Lamarin ya samo asali ne tun shekarar 2018 bayan makarantar ta hana ɗalibai mata Musulmai sanya hijabi. Daga bisani, wasu ɗalibai 11 tare da goyon bayan ƙungiyoyin kare muradun Musulmi suka kai ƙarar lamarin kotu.
A shekarar 2024, Babbar Kotun Jihar Oyo ta yanke hukuncin cewa hana ɗaliban sanya hijabi ya saɓa wa haƙƙinsu na addini, tare da bai wa masu ƙarar nasara.
Sai dai Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke wannan hukunci, inda mafi yawan alkalan da suka saurari shari’ar suka bayyana cewa makarantar ISI ba ta ƙarƙashin tsarin makarantun gwamnati saboda ba ta samun tallafin gwamnati kai tsaye.
Kotun ta kuma bayyana cewa wasu hukunce-hukuncen da suka gabata kan sanya hijabi sun fi shafar makarantun gwamnati, ba masu zaman kansu ba. Haka kuma ta ce ɗaliban sun amince da dokokin makarantar lokacin da suka shiga makarantar.
Duk da haka, ɗaya daga cikin alkalan da suka saurari ƙarar ya nuna rashin amincewa da hukuncin, yana mai cewa ɗaliban na da cikakken haƙƙin sanya hijabi kuma babu hujjar soke hukuncin da kotun farko ta yanke.
MPAC ta ce hukuncin ya ci karo da tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, musamman sashe na 38 da ke ba kowane ɗan ƙasa damar gudanar da addininsa cikin ’yanci.
Cibiyar ta yi gargaɗin cewa idan ba a sake duba hukuncin ba, zai iya zama wata kafa da za ta bai wa wasu makarantu damar takaita haƙƙin addinin ɗalibai Musulmai.
Haka kuma ta yi kira da a dakatar da aiwatar da hukuncin har sai an kammala matakan ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Koli, tare da roƙon Majalisar Dokoki ta Ƙasa da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya su ɗauki matakan da za su kare ’yancin ɗalibai wajen bayyana addininsu a makarantu.
MPAC ta kuma buƙaci ƙungiyoyin Musulmi da sauran masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam da su ci gaba da nuna damuwa kan lamarin, tana mai cewa kare ’yancin addini wani muhimmin ginshiƙi ne na dimokuraɗiyya da adalci.
