Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa inganta damar samun ilimi mai nagarta a faɗin ƙasar nan na daga cikin muhimman hanyoyin da za su taimaka wajen rage matsalar ta’addanci da rashin tsaro a Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a Kaduna yayin ƙaddamar da wata makarantar Kiristoci da aka gina a Unguwar Sunday da ke Sabon Tasha, a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
An samar da makarantar ne ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Tsaro ta DSS da wata ƙungiya mai zaman kanta, domin tallafa wa harkar ilimi da ci gaban al’umma.
A cewar ministan, samar da zaman lafiya mai ɗorewa ba zai yiwu ba sai an magance jahilci tare da bai wa matasa da sauran al’umma damar samun ilimi da abubuwan da za su inganta rayuwarsu.
Ya jaddada cewa ilimi na taka muhimmiyar rawa wajen hana matasa fadawa cikin ayyukan ta’addanci da sauran laifuffuka, saboda haka ya kamata a ci gaba da zuba jari a wannan fanni.
Ministan ya kuma yabawa Hukumar DSS bisa gudunmawar da take bayarwa wajen bunƙasa ilimi da ayyukan ci gaban al’umma, yana mai cewa irin waɗannan matakai na taimakawa wajen gina al’umma mai zaman lafiya da ci gaba.

