Daga cikin waɗanda aka tabbatar sun kamu har da wata mata ’yar ƙasar Faransa, wadda aka killace a birnin Paris bayan gwaje-gwaje sun nuna tana ɗauke da ƙwayar cutar.
Rahotanni sun ce ana ci gaba da kula da marar lafiyar a wani asibiti na musamman, inda jami’an lafiya suka tsaurara matakan kariya domin hana yaɗuwar cutar zuwa wasu mutane.
A gefe guda kuma, matukin jirgin ya fitar da wani saƙon bidiyo inda ya yaba wa fasinjojin jirgin bisa yadda suka nuna jajircewa da kwanciyar hankali yayin da suke fuskantar mawuyacin hali sakamakon barkewar cutar.
See less

