Sojojin Isra’ila sun bayyana cewa wasu daga cikin jami’ansu uku sun jikkata sakamakon wani hari da aka kai da jirgi mara matuƙi a kudancin ƙasar Lebanon.

Sojojin Isra’ila sun bayyana cewa wasu daga cikin jami’ansu uku sun jikkata sakamakon wani hari da aka kai da jirgi mara matuƙi a kudancin ƙasar Lebanon.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya afku ne a wani yanki da ke kusa da wuraren da ake yawan artabu tsakanin bangarorin biyu, lamarin da ya ƙara tayar da hankali game da yiwuwar faɗaɗar rikicin a yankin Gabas ta Tsakiya.

Sojojin Isra’ila sun tabbatar da aukuwar harin, amma ba su yi cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru ko irin raunukan da jami’an nasu suka samu ba. Sai dai sun ce an ɗauki matakan gaggawa domin kai dauki ga waɗanda suka jikkata.

Tun da farko dai ƙungiyar Hezbollah ta sanar da cewa mayaƙanta sun kai hari kan wani wurin da sojojin Isra’ila suka taru a yankin Tayyiba da ke kudancin Lebanon. Ƙungiyar ta ce harin ya yi nasara, inda ta yi zargin cewa an yi amfani da jirage masu saukar ungulu wajen kwashe sojojin Isra’ilar da suka samu raunuka daga yankin.

A wani labarin makamancin wannan kuma, Isra’ila ta ce ɗaya daga cikin sojojinta ya rasa ransa bayan wani hari da aka kai da jirgi mara matuƙi kusa da iyakar Lebanon a safiyar ranar yau. Wannan na nuna yadda hare-haren da ake kai wa a yankin ke ƙara tsananta a kullum.

A gefe guda kuwa, rahotanni daga Lebanon sun ce hare-haren saman da Isra’ila ke kai wa sun yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama. Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasar Lebanon ya ruwaito cewa jiragen yaƙin Isra’ila sun kai hari a ƙauyen Aba da ke arewacin ƙasar, inda mutane biyu suka mutu sannan wasu biyar suka jikkata.

Rahoton ya kuma bayyana cewa jiragen yaƙin Isra’ila sun sake kai wasu hare-hare biyu cikin ƙasa da awa guda a yankin Kafr Roman da ke kudancin Lebanon, lamarin da ya haddasa fargaba da tashin hankali a tsakanin mazauna yankin.

Masu sa ido kan al’amuran siyasa na ganin cewa rikicin tsakanin Isra’ila da Hezbollah na ci gaba da ƙara kamari, musamman bayan yawaitar hare-haren jirage marasa matuƙi da kuma luguden wuta ta sama daga bangarorin biyu.

Ana ci gaba da fargabar cewa idan ba a samu matakan sasanta rikicin ba, rikicin na iya bazuwa zuwa wasu sassan yankin Gabas ta Tsakiya, lamarin da zai iya haddasa babbar matsalar tsaro da ta jin ƙai ga fararen hula.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *