Hukumar EFCC ta bayyana matuƙar damuwa kan yadda harkar damfara ta yanar gizo, wadda aka fi sani da yahoo-yahoo, ke ƙara yawaita a tsakanin ɗaliban jami’o’in Najeriya.

Hukumar EFCC ta bayyana matuƙar damuwa kan yadda harkar damfara ta yanar gizo, wadda aka fi sani da yahoo-yahoo, ke ƙara yawaita a tsakanin ɗaliban jami’o’in Najeriya.

Shugaban hukumar, Olanipekun Olukoyede, ya bayyana cewa binciken da suka gudanar ya nuna cewa kusan ɗalibai 6 cikin 10 na jami’o’in ƙasar na da alaƙa da wannan aika-aika. Ya ce mafi yawan waɗanda ake kama da hannu a irin waɗannan laifuka ɗalibai ne.

Olukoyede ya yi wannan bayani ne a wani taron shugabannin jami’o’i da aka gudanar a Kano, inda ya nuna cewa matsalar na ƙara muni, har ma wasu ɗalibai na shiga harkokin cin hanci don samun sauƙi a makaranta.

A cewarsa, wannan al’amari na nuni da raunin tsare-tsare da rashin kulawa a wasu jami’o’i, musamman a fannin gudanar da harkokin kuɗi da tsaro.

Shugaban EFCC ya kuma kawo misalin wani samame da suka kai a Legas, inda aka kama mutane 792 da ake zargi da damfara ta ƙasashe da dama, kuma da dama daga cikinsu ɗalibai ne.

Haka kuma, ya nuna damuwa kan yawaitar abin da ake kira “Yahoo Plus”, inda ake haɗa damfara da wasu al’amuran tsafi.

Olukoyede ya bukaci shugabannin jami’o’i su ɗauki matakan gaggawa domin dakile wannan matsala, ciki har da amfani da fasahar zamani kamar AI wajen gano zamba da inganta tsaro.

Ya jaddada cewa rashin gaskiya a harkokin kuɗi na iya lalata tsarin ilimi, yana mai cewa ingancin jami’a yana da alaƙa kai tsaye da tsaron ƙasa.

A ƙarshe, ya buƙaci a ƙara horas da ma’aikata a fannoni kamar tsaron yanar gizo da fasahar zamani, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jami’o’i da hukumomin yaƙi da cin hanci domin shawo kan wannan barazana

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *