Gwamna Abba ya aike da  sunan Murtala Garo don tantancewa a matsayin Mataimakinsa.

Gwamna Abba ya aike da sunan Murtala Garo don tantancewa a matsayin Mataimakinsa.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ɗauki matakin cike gurbin mataimakin gwamna ta hanyar miƙa sunan Murtala Sule Garo ga Majalisar Dokokin Jihar domin tantancewa da amincewa.

Wannan mataki na zuwa ne bayan tsohon Mataimakin Gwamna, Abdussalam Gwarzo, ya ajiye muƙaminsa a ranar 27 ga Maris, 2026, lamarin da ya bar gurbin a bude.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mustapha Muhammad, ya fitar, an bayyana cewa wannan naɗi ya bi ƙa’idojin kundin tsarin mulki, musamman sashe na 191(3), wanda ke bai wa gwamna damar zaɓar sabon mataimaki idan aka samu gurbi.

Bayan tuntuba da manyan masu ruwa da tsaki a siyasar jihar, Gwamna Abba ya nemi goyon bayan majalisar domin tabbatar da Garo a matsayin sabon mataimakinsa.

Murtala Sule Garo, wanda ke da shekaru 48, ya shahara a fagen siyasa, inda ya shafe sama da shekaru 20 yana riƙe da muƙamai daban-daban. Daga cikin mukaman da ya taɓa riƙewa akwai shugaban ƙaramar hukuma, kwamishina, da kuma shugaban ALGON a Kano.

Har ila yau, ya kasance ɗan takarar mataimakin gwamna a jam’iyyar APC a zaɓen 2023, abin da ya ƙara masa ƙwarewa a harkokin shugabanci.

Gwamnatin Kano ta bayyana cewa wannan naɗi wani ɓangare ne na ƙoƙarin inganta tsarin mulki da ƙarfafa jagoranci a jihar.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *